<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Ya Ubangijinmu, Kalmarka Ta Dauwama LW62</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ya Ubangijinmu, Kalmarka ta dauwama
 Wajib ne a gaskata, a kuma karƃe ta.

[V2]
 2) Idan maƙiyanmu suna tsananta mana,
 Maganar cetonka ita ce ƙarfinmu.

[V3]
 3) In wahala ta zo, ko masifa ta taso,
 Haskenka zai bishe mu, za ya kiyaye mu.

[V4]
 4) Wa ya san misalin murna mafificiya
 Ta miƙa bishararka zuwa mutanenka.

[V5]
 5) Jinƙanka ke ba da taimako ga masu rai,
 Maganarka ta'aziyya ga wanda ke mutuwa.

[V6]
 6) Mu da muka gane tsarkin wannan Kalma,
 Sai mu ƙaunace ka, don kullum mu bi ka.</lyrics>
<hymn_number>62</hymn_number>
</song>